(ABNA24.com) Gwamnatin hadaddiyar daular larabawa ta bukaci kasar Iran ta dawo kan teburin tattaunawa da manya-manyan kasashen duniya da kuma kasashen yankin don sake farfado da tattalin arzikin kasarta.
Kamfanin dillancin labaran reuters ya nakalto Anwar Gargash karamin ministan harkokin wajen kasar UAE yana fadar haka a jiya Lahadi a birnin Abuzabi.
Anwar Gargash ya kara da cewa dole ne Iran ta dawo kan teburin tattaunawa wanda zai hada da manya-manyan kasashen duniya da kuma kasashen yankin. Inda a wannan karon za’a tattauna batun shirin iran na makamashin nukliya da kuma na makamanta masu linzami.
Kasar Amurka ta fice daga yerjejeniyar nukliyar kasar Iran ta shekara ta 2015 ne a shekara ta 2018, sannan ta maida dukkan takunkuman da aka daukewa Iran bayan yerjejniyar, da kuma kari.
Amurka tana bukatar Iran ta dawo kan teburin tattaunawa da don bude sabuwar tattaunwa da Amurka da kuma sauran manya-manyan kasashen duniya.
/129
12 Nuwamba 2019 - 05:15
Lambar labari: 987364
Gwamnatin hadaddiyar daular larabawa ta bukaci kasar Iran ta dawo kan teburin tattaunawa da manya-manyan kasashen duniya da kuma kasashen yankin don sake farfado da tattalin arzikin kasarta.